Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia (MASISIJA) ta gudanar da muhimmin taro domin sanin makamar aikinta na yada da'awar maluman muslunci.
Ranar laraba 10/06/2020 wasu daga cikin jagororin wannan kungiya suka yi taro inda suka tattauna akan muhimman abubuwanda zasu taimaka masu a fagen aikinsu.
Watanni biyu da suka gabata kungiyar MASISJA ta shirya wata muhadara mai taken "Tambayoyi da Amsoshi" ta tsawon sati shidda (6) wadda Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia ke gabatarwa.
A cikin ikon Allah, an gabatar da ta tsawon makonni hudu (4) sai cutar Covid-19 ta billo wanda hakan yasa hukuma ta dakatar da dukkanin wani taro domin samun kariya daga cutar.
To Allah da ikonsa kuma bayan cutar ta lafa a jihar Katsina, yanzu an cigaba da harakoki kamar yadda aka saba.
Saboda haka ne kungiyar MASISJA, a karkashin wannan mitin, ta shirya tsaf domin cigaba da muhadarar tsawon sati biyu wadda mata ne kadai za ayi wa banda maza kamar yadda sanarwa ta gabata a babban shafin kungiyar.
Taron na yau, ya samu halartar:
1. Abdulazeez Salisu Yusuf
(Assistant Secretary General)
2. Bashir Mudi Yawale
(Organizing Secretary)
2. Auwal Shu'aibu
(Assistant Organizing Secretary)
3. Safwan Sirajo Agaji
(Financial Secretary)
4. Umar Abdulhadi Jibia
(Treasurer)
5. Umar Lurwan
(Public Relation Officer I)
6. Hassan Ibrahim Sabi'u
(Director Protocol)
7. Usman Lurwan
(Member)
Sai dai shugaba Abdulrazak Ahmad Jibia da mataimakinsa Babangida Abdulmajid sun bada uzurin rashin halartarsu.
Muna addu'a Allah yasa Albarka Amin.




Comments