Skip to main content

BARISTA IBRAHIM SABI'U JIBIA YA YI KIRA GA 'YAN KASUWA DASU SAUKAKA FARASHI A CIKIN WATAN AZUMI:

Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia


Mataimakin shugaban majalissar malamai ta kungiyar Izala dake tarayyar najeriya Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u Jibia ya yi kira ga 'yan kasuwa dasu saukaka farahin kowane irin nau'in kaya musamman a cikin watan azumin ramadana.

Ya ce ana bukatar kowane musulmi yayi koyi da shugaban halittu Annabi Muhammad (S.A.W) wajen yawaita taimako da bada tallafi ga Marayu, Gajiyayyu, da sauran mabukata, domin a cikin watan azumi ne Allah ke gafartawa bayinsa.

Ya kara da cewa yana da kyau 'yan kasuwanmu su kara saukaka farashi hatta wandanda ba musulmai ba su amfanu da romon azumin watan ramadana, saboda manzom tsira (A.S) ya kasance mai fadada kyauta a acikin watan azumi duk da cewa shi mutum ne mai yawan kyauta a koda yaushe.

Sannan ya yi kira ga masu rike da mukami na siyasa dana sarauta gami da attajirai cewa suji tsoron Allah su jajirce wajen taimakawa na kasa dasu domin karfin da Allah yayi masu.

Kazalika suma talakawa ba'a barsu a baya ba, yana da kyau suma suyi sadaka daidai kwargwadon abinda Allah ya hore masu koda kwayar dabino ne.

Daga karshe ya bayyana cewa a cikin watan azumi ne ake daure dukkanin sheidanu masu tauye bayi daga bautar Ubangijinsu, to saboda haka yana da kyau a cikin watan azumi mu sakankance masu bautawa Ubangijin fiye da kowane lokaci.

Shehin malamin ya yi wannan kira ne makon daya gabata a harabar gidansa dake unguwar sarki kusa da fadar mai girma sarkin arewan Katsina, hakimin Jibia.

Muna rokon Allah madaukakin sarki ya kawo mana rangwame, kuma ya bamu ikon yin amfani da wannan nasiha Amin.

Comments

Popular posts from this blog

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia ta gudanar da taro domin sanin makamar aiki

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia (MASISIJA) ta gudanar da muhimmin taro domin sanin makamar aikinta na yada da'awar maluman muslunci.  Ranar laraba 10/06/2020 wasu daga cikin jagororin wannan kungiya suka yi taro inda suka tattauna akan muhimman abubuwanda zasu taimaka masu a fagen aikinsu.  Watanni biyu da suka gabata kungiyar MASISJA ta shirya wata muhadara mai taken "Tambayoyi da Amsoshi" ta tsawon sati shidda (6) wadda Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia ke gabatarwa.  A cikin ikon Allah,  an gabatar da ta tsawon makonni hudu (4) sai cutar Covid-19 ta billo wanda hakan yasa hukuma ta dakatar da dukkanin wani taro domin samun kariya daga cutar.  To Allah da ikonsa kuma bayan cutar ta lafa a jihar Katsina, yanzu an cigaba da harakoki kamar yadda aka saba.  Saboda haka ne kungiyar MASISJA, a karkashin wannan mitin, ta shirya tsaf domin cigaba da muhadarar tsawon sati biyu wadda mata ne kadai za ayi wa banda maza ka...

MA'ANAR SHI'A DA MANUFOFINSU (001)

Wannan raddi ne zuwa ga Ado Lamama game da shirmenda yayi a matsayin raddi zuwa ga Malamin Sunnah Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia.  Daga: Sheikh Mustafa Mansur Jibia Da farko Inaso in fara da bayani akan minene shia.  Hakika shi'a kishiyar sunnah ce ta fuskar akida.  Sunnah tana nufin addinin da manzon Allah Ya zo dashi kuma mai yin irinsa ya yarda da sahihancin sayyidnah Abubakar, umar, Uthman da Aliyu, tareda gamsuwa da tsarkin dukkanin matayen manzon Allah, gami da yarda da cewa duk sahabbai adalai NE. To wannan shine atakaice maganar Sunnah, kuma kishiyar hakan to shine shia, kamar kudurce cewa sayyidnah Abubakar, umar da uthman mutanen banza ne kuma yan wuta, sannan matan manzon akwai na banza acikinsu, musamman Nana Aisha Da Nana Hafsah sannan hadi da kafirta wani adadi na sahabban manzon Allah. To idan masu sauraro Sun fahinci banbance babancen to akan hakane zan gina raddi na akan rubutun da akayi.  Don haka a biyo don ...

Ya kamata a dinga tabbatar da sahihancin labari kafin a yada - Sheikh Sabi'u Jibia

Sheikh Ibrahim Sabi'u ya yi kira ga 'yan Social Media da su dinga tabbatar da Ingancin labari kafin su yada shi. Mataimakin shugaban majalissar ta kungiyar JIBWIS dake tarayyar najeriya Sheikh (Barr) Ibrahim Sabi'u Jibia, a yayin da yake gabatar da khudbar sallar juma'a yayi kira  ga masu amfani da kafafen sadarwar zamani (Social Media) su guji yada sharri da labarin karya. Ya kara da cewa: yana da kyau mutane  su dinga bincike domin tabbar da ingancin labari kafin su yada shi don gudun aikata abinda zai sa mutum ya wayi gari yana mai ladama game da abinda ya aikata. Kazalika ya karanto ayoyi daga  alqur'ani mai girma da hadisan Annabi (S.A.W) wadanda suke magana akan haramcin yin irin wannan mummunan aiki, wanda yin haka babban abin kyama ne a wajen Allah madaukakin sarki. A cewarsa tsawon lokaci da ya gabata akan samu batagarin malamai ne masu karantar da hadisan karya a yayin da suke karantar da dalibansu, amma yanzu zamani ya canza, kana kwance a gida za kai ta ...