Skip to main content

SHEIKH BARR. IBRAHIM SABI'U JIBIA YA JA HANKULLAN 'YAN UWA MUSULMI DA SUBI UMARNIN SHUGABANNI:

Mataimakin Shugaban Majalissar Malamai ta kungiyar JIBWIS dake tarayyar najerya, Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u "Sarkin Malaman Jibia", ya ja hankullan 'yan uwa musulmi da subi umarnin shugabbani madamar bai saba wa addinin musluncii ba.

Ya ce bai kamata talakawa/mabiya suyi jayayya da abinda hukuma tayi umarni a matsayin maslaha ga al'umma ba.

Ina jawo hankulla musamman na 'yan uwa Malamai da Almajirai cewa ita tafiya ta addinin muslunci dole sai anyi biyayya ga Allah da Manzonsa da kuma hukuma, da abinda yake maslaha ga al'umma.

Idan aka umarcemu da aikata wani abu ko kaurace masa, to kada ya zamo matsala, saboda duk abinda aka ce kada ayi a wannan yanayin magana ce dake nuna ba'a bukatar taron jama'a a wurin.

Maganar sallar juma'a da aka  a dakatar da yinta a masallamatan juma'a ba matsala bane saboda babu Wanda aka hana yaje gida yayi.

Saboda haka ina kara jawo hankullan 'yan uwa na Almajirai cewa kada mutum ya dauka idan yayi karatu "ya zama malamin komai; dole ne akwai abinda bakai za a tambaya ba sai wanda yayi karatu a fannin.

Duba da halin da muke ciki na cutar korona (Covid-19), ina kira ga mutane a fannin lafiya abar wa malaman lafiya aikinsu, saboda daga gare sune gwamnatoci ke karbar fatawoyi kan yadda za a kawo karshen yaduwar wannan cuta da kuma kare rayukan al'umma da kamuwa da ita.


Yana da kyau kowa ya tsaya bakin iliminsa, kada malami ya dauka cewa idan aka saka doka banda shi, domin karatu daban kuma bin doka ma daba.

Wajibi ne ga malamai subi doka kamar yadda kowa yake bin ta, hasalima su ake kyautatawa zaton cewa sune masana doka kuma su suka san darajar masu doka, saboda haka ya kamata malamai su bita fiye da kowa.

Sannan kada malamai su biyewa  mazuga, su afka ga fitina, idan ance ayi abu kaza " AYI" idan kuma akayi hani to "A BARI. Mun sani babu wanda za ace kada yayi sallah.

Dakatar da yin Sallar Juma'ar nan fa da ace mutane sun wayi gari ana ruwan sama har lokacin sallar yayi, da mutune ba zasu ce dole sai sunje masallaci ba a gida ma za su iya tsayawa suyi sallar azhur. Kamar yadda matafiyi zai ga ana sallar juma'a akan hanyarsa ta zuwa wani gari ba zai yita ba har sai idan ya isa gida shima yayi sallar azhur.

Daga karshe ina nasiha a garemu, masu zuga wasu don Allah su daina, da fatan Allah ya kawo mana karshen wannan Annoba Amin.

****
Shehin malamim ya isar da wannan sako ne akan mimbari yayin khudbar sallar Juma'a.

Danna wannan LINK din dake kasa domin sauke AUDIO akan wayoyinku
👇👇👇👇👇
https://web.darulfikr.com/s/87402

Ku cigaba da kasancewa damu a shafukanmu na yanar gizo👇

Website:
www.masisjanigeria.blogspot.com
Email:
masisjanigeria@gmail.com
Whatsapp:
https://wa.me/2347044677956
_________________
Masisja Nigeria
17/04/2020

Comments

Popular posts from this blog

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia ta gudanar da taro domin sanin makamar aiki

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia (MASISIJA) ta gudanar da muhimmin taro domin sanin makamar aikinta na yada da'awar maluman muslunci.  Ranar laraba 10/06/2020 wasu daga cikin jagororin wannan kungiya suka yi taro inda suka tattauna akan muhimman abubuwanda zasu taimaka masu a fagen aikinsu.  Watanni biyu da suka gabata kungiyar MASISJA ta shirya wata muhadara mai taken "Tambayoyi da Amsoshi" ta tsawon sati shidda (6) wadda Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia ke gabatarwa.  A cikin ikon Allah,  an gabatar da ta tsawon makonni hudu (4) sai cutar Covid-19 ta billo wanda hakan yasa hukuma ta dakatar da dukkanin wani taro domin samun kariya daga cutar.  To Allah da ikonsa kuma bayan cutar ta lafa a jihar Katsina, yanzu an cigaba da harakoki kamar yadda aka saba.  Saboda haka ne kungiyar MASISJA, a karkashin wannan mitin, ta shirya tsaf domin cigaba da muhadarar tsawon sati biyu wadda mata ne kadai za ayi wa banda maza ka...

MA'ANAR SHI'A DA MANUFOFINSU (001)

Wannan raddi ne zuwa ga Ado Lamama game da shirmenda yayi a matsayin raddi zuwa ga Malamin Sunnah Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia.  Daga: Sheikh Mustafa Mansur Jibia Da farko Inaso in fara da bayani akan minene shia.  Hakika shi'a kishiyar sunnah ce ta fuskar akida.  Sunnah tana nufin addinin da manzon Allah Ya zo dashi kuma mai yin irinsa ya yarda da sahihancin sayyidnah Abubakar, umar, Uthman da Aliyu, tareda gamsuwa da tsarkin dukkanin matayen manzon Allah, gami da yarda da cewa duk sahabbai adalai NE. To wannan shine atakaice maganar Sunnah, kuma kishiyar hakan to shine shia, kamar kudurce cewa sayyidnah Abubakar, umar da uthman mutanen banza ne kuma yan wuta, sannan matan manzon akwai na banza acikinsu, musamman Nana Aisha Da Nana Hafsah sannan hadi da kafirta wani adadi na sahabban manzon Allah. To idan masu sauraro Sun fahinci banbance babancen to akan hakane zan gina raddi na akan rubutun da akayi.  Don haka a biyo don ...

Ya kamata a dinga tabbatar da sahihancin labari kafin a yada - Sheikh Sabi'u Jibia

Sheikh Ibrahim Sabi'u ya yi kira ga 'yan Social Media da su dinga tabbatar da Ingancin labari kafin su yada shi. Mataimakin shugaban majalissar ta kungiyar JIBWIS dake tarayyar najeriya Sheikh (Barr) Ibrahim Sabi'u Jibia, a yayin da yake gabatar da khudbar sallar juma'a yayi kira  ga masu amfani da kafafen sadarwar zamani (Social Media) su guji yada sharri da labarin karya. Ya kara da cewa: yana da kyau mutane  su dinga bincike domin tabbar da ingancin labari kafin su yada shi don gudun aikata abinda zai sa mutum ya wayi gari yana mai ladama game da abinda ya aikata. Kazalika ya karanto ayoyi daga  alqur'ani mai girma da hadisan Annabi (S.A.W) wadanda suke magana akan haramcin yin irin wannan mummunan aiki, wanda yin haka babban abin kyama ne a wajen Allah madaukakin sarki. A cewarsa tsawon lokaci da ya gabata akan samu batagarin malamai ne masu karantar da hadisan karya a yayin da suke karantar da dalibansu, amma yanzu zamani ya canza, kana kwance a gida za kai ta ...