Ina kira ga shugabannin jiha da sauran masu hanyar ganawa da shugaban kasa, da 'yan jaridu da ma'aboda hanyoyin sadarwa, don Allah ku isar da wannan sako zuwa ga shugaban kasar najeriya.
~Sheikh Barr Ibrahim Sabi'u Jibia
Talakawa suna cikin damuwa da tashin hankali, kullum kashe mu ake, ana kwashe mana dabbobi, kuma ana yin garkuwa damu. An kwace mana shanu, taimaki, awaki.
Duk an gama talauta talakawanmu yanzu har an kai matakin da hatta Jakkai basu bari ba, wani lokacin ma da buhunna suke zuwa kauyuka suna kwashe mana kaji da zabbi.
Yanzu talakawan mun daina tunanin damina tazo muyi noma, fafutikarmu kawai "neman wurin da zamu je mu tsira" fatanmu mutuncinmu dana iyalanmu ya tsira.
Saboda haka ina kira ga masu hali su isar da kukanmu ga shugaban kasa, al-ummar najeriya muna cikin damuwa, musamman a jihar Katsina.
***
Zaku iya sauraren dukkanin jawaban malamin kai tsaye.
Danna wannan LINK din dake a kasa domin saukewa a wayoyinku👇
Daure ku saurara domin jin yadda malamin yayi jawabai masu mahimmanci tare da nuna alhininsa game da halin da kasar najeriya take ciki.
Muna addu'a Allah madaukakin sarki ya kawo mana zaman lafiya Amin.

Comments