Wannan raddi ne na uku zuwa ga Ado Lamama game da shirmenda yayi a matsayin raddi zuwa ga Malamin sunnah Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia.
Daga: Sheikh Mustafa Mansur Jibia
Ado ya ce: Saed bn musayyib shima dan shia ne kuma shine shugaban masu tafsiri na tabi'ai.
To ni kuma nace sam ba dan shia ba NE kuma ma karya ce shi ba malamin tafsiri ba NE, ko da yake shi lamama bai fadi madogararsa ba, amma ni ku biyo ni ku ga tawa madogarar.
Saed bn musayyib dai haifaffen garin madina NE, kuma tabi'i NE, daya ne daga cikin maruwaita hadisin manzon Allah, kuma daya daga cikin masana fiqhun madina guda bakwai daga cikin tabi'ai, anayi masa laqabi da babban malamin madina kuma shugaban tabi'ai. Idan mai karatu dalibin ilmi ne ko nan na tsaya zai fahinci lalle Saed bn musayyib sunni NE, saboda kasancewarsa mutumin madina kuma mahaifinsa sahabi haka ma Kakansa.
Bugu da kari acikin madina ne Ya kare rayuwarsa.
Ga sahabbanda yayi karatu a wurinsu: zaid bn thabit, saad bn abi waqqas, Abdullahi bn Abbas, Abdullahi bn Umar, Nana Aisha, ummu Salamah, Aliyu bn Abi dalib, Suhaibu Rumiy, Muhammad bn Maslamah, Abu Hureira sai Umar bn khattab. Saed bn musayyib saboda shakuwarsa da Abu Hureira har diyarsa ya aura, wanda Wannan ya basa damar kwankwadar ilmin hadisi a wurin sirikinsa.
Duk wannan bayanan nawa ba nina kagesu ba Imamu Zahabi ne Ya fadesu a littafinsa na siyaru aalamin nubalaa.
Sannan mai wahbatuz zahiyliy ga abinda yake Cewa akan salon binciken fiqh na Saed bn musayyib :إعتمد سعيد بن المسيب في منهجه الفقهي على القرآن والسنة والاجماع والقياس فإن لم يجد حكما تخير من أقوال الصحابة.
Ma'ana Saed bn musayyib Ya dogara ne a wurin tsarinsa na fiddo hukuncin fiqhu akan Alkur'ani da sunnah da Ijmai da kuma Qiyasi.
To naji dan shine zai kafa hujja da Sunnah? Sannan kuma Imamu zahabiy a dabaqatul kubrah ga abinda yace kan Saed bn musayyib :كما امتاز سعيد بن المسيب بميزة القدرة في تعبير الرؤى ألتي اكتسبها من اسماء بنت ابي بكر الصديق ألتي أخذتها عن ابيها.
Ma'ana kamar yadda Saed bn musayyib Ya fifita da fifikon iko kan fassarar mafarki Wanda Ya koya daga Asmau bintu Abubakar Wanda ita ma ta koya daga babanta.
Jamaa ku gane mani hanya! Dan Shi'a zai je gidan sayyidnah Abubakar neman ilmi?
Daga karshe don kada in tsawaita, karya mai lamama keyi da yace Saed bn musayyib shine shugaban masu tafsir na tabi'ai, amma ga maganar imamu zahaby ورغم علمه بالحديث النبي الا ان سعيد بن المسيب كان يعرف عن تفسير القرآن كما كان يحب الشعر وكان لا ينشده. Maana duk da dinbin ilminsa na hadisin Annabi sai dai Saed bn musayyib Ya kasance yana dari dari da tafsirin Alkur'ani kamar yadda yana sauraron wake amma shi baya rerawa.
Da yan wadannan kalmomin ne nike fahimtar Saed bn musayyib Sunni ne ba shia ba, duba da an haifeshi ne run duniya na cikin hayyacinta hijra shekara 15 kuma Ya rasu a shekara ta 95. سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك
MASISJA NIGERIA
31/05/2020

Comments