Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia, tsohon sakataren shari'a na jihar Katsina, ya jajantawa al'ummar jihar a bisa iftala'in 'yan bindiga, barayin dabbobi, dake addabarsu ba dare ba rana.
Sanin kowane cewa tuntuni wadannan batagari suke kai hare-hare a bangarori daban-daban na jihar, musamman a yankunan Batsari, Kankara, Dan-musa da sauransu.
Ya kara da cewa hatta ranar laraba 6 gawatan mayun shekara ta 2020, labari ya zo masu inda aka shaida masu cewa yan ta'addar sun shiga kauyen zandam dake karamar hukumar Jibia. Wanda wani lokaci daya gabata ma sun taba shiga garin inda suka jikkita wasu, suka tafi da dabbobinsu.
Barista Sabi'u Jibia yayi kira ga Al'ummar kan su dukufa dayin addu'o'i a cikin wannan wata na ramadana, a lokacin sahur da lokacin shan ruwa, da kuma lokacin da ake sallah musamman a cikin sujjada. Ya ce kada a gajiya, domin addu'ar mu'umini bata faduwa kasa.
Tsohon Sakataren Shari'ar Ya yi kira ga Gwamnatoci da suji tsoron Allah!
Ya ce tabbas 'yan ta'addar nan basu fi kafin gwamnati ba, saboda akwai wasu munafukai a cikinsu wadanda dasu ake hada kai ana wannan ta'addancin.
Daga karshe malamin yayi addu'ar nemawa Al'ummar zaman lafiya, tare da addu'ar nema masu sakayyar Allah akan zaluncin da ake yi masu.
Muna addu'a Allah ya kawo mana zaman lafiya Amin.
*****
Danna wannan LINK din dake a kasa domin sauke sautin wayoyinku👇
AYI SAURARO LAFIYA

Comments