- Malamin addinin muslunci, Alqali Sheikh Lawal Musa Muhammad Jibia, ya yi kira ga gwamnatin kasar najeriya data maida hankalinta akan ma'sala ta tsaro.
Daga Abdulrazak Ahmad Jibia
- Duba da halinda al'ummar najeriya suka tsinci kansu a ciki na ta'addancin 'yan bindiga musamman a jihar Katsina, inda suke shiga gari su karkashe na kashewa kuma suyi garkuwa da mutane, tare da kwashe masu dabbobi gami da yiwa matan aure da 'yan mata fyade.
- A sakamakon abin ya kaisu makura, yasa a cikin wannan makon al'umamar gari da karkara a inda abin ke faruwa suka fito kwai da kwarkwata, sukayi zanga-zangar lumana domin nunawa duniya halin da suke ciki koda zasu samu dauki na musamman daga gwamnati.
- Wannan dalilin ne yasa: Sheikh Lawal Musa Jibia, ya yi takaitacciyar fadakarwa inda ya bayyana cewa "Ya kamata gwamnatin najeriya ta maido hankalinta zuwa sha'anin tsaro domin shine babbar damuwar talakawan kasar".
- Malamin ya kara da cewa: Abinda ya faru na zanga-zangar da al'ummar karamar hukumar Jibia sukayi kadan ne, saboda da haka ya zama wajibi gwamanti ta dauki kwakkwaran mataki akan tsaro, in ba haka ba wataran za'a wayi gari Al'ummar najeriya suyi boren da hatta garin Abuja inda fadar shugaban kasa take sai ya gagari kowa shiga.
- Danna wannan Link din dake a kasa domin kallon cikakken bidiyo mai kunshe da jawabin malamin
- 👇👇👇👇👇
- https://youtu.be/yjXkuoxy70E
- Ayi kallo lafiya

Comments