Skip to main content

A SHIRYE NAKE INYI MUQABALA DA KOWA DOMIN KARE MARTABAR MUSLUNCI - Sheikh Lawal Musa Jibia

Edin karamar sallar bana 1441/2020 da ya gabata, Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia mataimakin shugaban kwamtin Da'awah na kungiyar JIBWIS dake karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina, shine ya gabatar da wa'azi kafin isowar liman.


A cikin nasihohinsa, ya janyo hankullan 'yan uwa musulmai da yi masu nasiha game da batanci da jifar da aka yiwa Mai girma sarkin musulmin najeriya a jiharsa ta Sokoto game da mas'alar ganin Wata, wanda hakan ya sabawa Shari'a ta addinin muslunci.

Saboda haka ne wasu masu karancin karatu ke faman cecekuce domin a cikin nasihar ya bayyana masu irin wannan mummunan aiki a matsayin jahilai.

Wannan dalilin ne yasa wasu tsiraru sukai tayi masa raddin jahilci suna yadawa a kafafen yada labarai.

kafin malamin yace komai an samu wasu maluma na sunnah wadanda suka yi raddi na ilimi zuwa ga masu kalubalantar malamin game da gaskiyar da ya fada wacce maluman sunnah MA sun tafi akanta.

Daga bisani shehin malamin shima ya tofa albarkacin bakinsa, inda yace:

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته
Ni Lawal musa bana tababar abinda na fada gameda maganar da nayi  a yayin da nake wa'azi ranar Idin karamar sallah a gaban mutane.

Jama'a yaya zaku biyewa Adamu lamama aita magan-ganu marassa manufa? Shin wanda ya zargi matar Manzon Allah, yaci mutuncin Abubakar, da umar, da Hafsat yar Sayyidina umar, idan ance masa Jahili ko mutumin Banza shine Rashin Hikima??

 To shi mai wannan maganar da yake kare lamama kodai shima Dan Shi'ar ne ko kuma yana da wani ra'ayi nasa!

 Duk mai bukatar wata Mukabala ko wata Tattaunawa,  yazo muyi don mufahinci juna, maida martani a cikin wani group ba zai wadatar ba.

Nagode, dan Uwanku a musulunci Lawal musa.

***
Wannan shine Jawabin malamin.

 Dan fatan Allah ya kara hada kan musulmai Amin.

MASISIJA NIGERIA
10/06/2020

Comments

Popular posts from this blog

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia ta gudanar da taro domin sanin makamar aiki

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia (MASISIJA) ta gudanar da muhimmin taro domin sanin makamar aikinta na yada da'awar maluman muslunci.  Ranar laraba 10/06/2020 wasu daga cikin jagororin wannan kungiya suka yi taro inda suka tattauna akan muhimman abubuwanda zasu taimaka masu a fagen aikinsu.  Watanni biyu da suka gabata kungiyar MASISJA ta shirya wata muhadara mai taken "Tambayoyi da Amsoshi" ta tsawon sati shidda (6) wadda Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia ke gabatarwa.  A cikin ikon Allah,  an gabatar da ta tsawon makonni hudu (4) sai cutar Covid-19 ta billo wanda hakan yasa hukuma ta dakatar da dukkanin wani taro domin samun kariya daga cutar.  To Allah da ikonsa kuma bayan cutar ta lafa a jihar Katsina, yanzu an cigaba da harakoki kamar yadda aka saba.  Saboda haka ne kungiyar MASISJA, a karkashin wannan mitin, ta shirya tsaf domin cigaba da muhadarar tsawon sati biyu wadda mata ne kadai za ayi wa banda maza ka...

MA'ANAR SHI'A DA MANUFOFINSU (001)

Wannan raddi ne zuwa ga Ado Lamama game da shirmenda yayi a matsayin raddi zuwa ga Malamin Sunnah Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia.  Daga: Sheikh Mustafa Mansur Jibia Da farko Inaso in fara da bayani akan minene shia.  Hakika shi'a kishiyar sunnah ce ta fuskar akida.  Sunnah tana nufin addinin da manzon Allah Ya zo dashi kuma mai yin irinsa ya yarda da sahihancin sayyidnah Abubakar, umar, Uthman da Aliyu, tareda gamsuwa da tsarkin dukkanin matayen manzon Allah, gami da yarda da cewa duk sahabbai adalai NE. To wannan shine atakaice maganar Sunnah, kuma kishiyar hakan to shine shia, kamar kudurce cewa sayyidnah Abubakar, umar da uthman mutanen banza ne kuma yan wuta, sannan matan manzon akwai na banza acikinsu, musamman Nana Aisha Da Nana Hafsah sannan hadi da kafirta wani adadi na sahabban manzon Allah. To idan masu sauraro Sun fahinci banbance babancen to akan hakane zan gina raddi na akan rubutun da akayi.  Don haka a biyo don ...

Ya kamata a dinga tabbatar da sahihancin labari kafin a yada - Sheikh Sabi'u Jibia

Sheikh Ibrahim Sabi'u ya yi kira ga 'yan Social Media da su dinga tabbatar da Ingancin labari kafin su yada shi. Mataimakin shugaban majalissar ta kungiyar JIBWIS dake tarayyar najeriya Sheikh (Barr) Ibrahim Sabi'u Jibia, a yayin da yake gabatar da khudbar sallar juma'a yayi kira  ga masu amfani da kafafen sadarwar zamani (Social Media) su guji yada sharri da labarin karya. Ya kara da cewa: yana da kyau mutane  su dinga bincike domin tabbar da ingancin labari kafin su yada shi don gudun aikata abinda zai sa mutum ya wayi gari yana mai ladama game da abinda ya aikata. Kazalika ya karanto ayoyi daga  alqur'ani mai girma da hadisan Annabi (S.A.W) wadanda suke magana akan haramcin yin irin wannan mummunan aiki, wanda yin haka babban abin kyama ne a wajen Allah madaukakin sarki. A cewarsa tsawon lokaci da ya gabata akan samu batagarin malamai ne masu karantar da hadisan karya a yayin da suke karantar da dalibansu, amma yanzu zamani ya canza, kana kwance a gida za kai ta ...