Yau Lahadi 05/07/2020 Sheikh Barr. Ibrahim Sabiu ya yi shekara daya a matsayin "Sarkin Malaman Jibia".
Tarihi ya nuna cewa tun farkon kafuwar masarautar Jibiya ba'a taba bada mukamin Sarkin Malamai ba sai a shekarar data gabata, inda aka dauko daya daga cikin Malaman da ke fadi tashi don ganin addinin Muslunci ya samu gindin zama a fadin duniyar nan.
A shekarar data gabata ne, Mai girma Sarkin Arewan Katsina-Hakimin Jibia Alhaji Rabe Rabi'u Ibrahim, ya bada wannan mukami ga Malam Ibrahim Sabi'u, wanda akayi bikin nadin sarautar a ranar juma'a 05/07/2019 da misalin karfe 10 na safe, a fadar mai masarautar dake Jibiya.
Barrister Ibrahim Sabi'u, ya kasance dan uwa na jini ga Sarkin Arewan Katsina-Hakimin Jibia Alhaji Rabe Rabi'u Ibrahim, wannan alaka ta nuna cewa 'ya'yan wa da kanine, Sarkin Malamai yaya ne ga Hakimin na Jibiya.
An nada Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u a matsayin Sarkin Malamai ne biyo bayan kasancewarsa shararren malamin addinin muslunci mai da'awah fadin kasar najeriya da sauran kasashen ketare.
Kuma mutum ne mai hakuri da tawakkali da tsoron Allah, mutum ne wanda baya gudun mutane kuma ya kasance mai son ganin Al'umma sunci gaba, kazalika mutum ne wanda a koda yaushe yake kokarin nuna wa mutane mahimmancin dogaro ga Allah da Addu'a, kuma aduk lokacinda zai hau mimbarin khudubar sallar juma'a baya gushewa face yaja nunawa Al'umma mahimmancin Tuba zuwa ga Allah (Istigfar) da salatin Annabi.
Malam mutum ne mai yiwa Al'umma wasilci da su kasance masu gaskiya da rikon amana aduk inda suka tsinci kansu, sannan ya kasance mai gudun duniya (Tawadhu'u) kuma mai fadawa kowa gaskiya komai rashin dadinta.
Babu shakka wannan mukami nasa na Sarkin Malamai an bayar dashi a inda ya dace, domin ya taimaki Al'ummar musulmi ta bangarori da dama, musamman yadda malamin ya sadaukar da rayuwarsa domin kare martabar addinin muslunci da musulmai bakidaya.
Muna rokon Allah madaukakin sarki ya karawa rayuwarsa Albarka, ya albarkaci zuriyyarsa, yasa Aljanna tazam makoma a gare shi.
Muna Addu'a Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana domin anfanuwar addinin muslunci.




Comments