Skip to main content

MA'ANAR SHI'A DA MANUFOFINSU (002)

Raddi na biyu zuwa ga Ado Lamama game da shirmenda yayi a matsayin raddi zuwa ga Malamin sunnah Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia.
Daga: Sheikh Mustafa Mansur Jibia 


Ado ya ce: sayyidnah Aliyu dan shia  ne, ni kuma nace sam babu alaka tsakanin sayyidnah Aliyu da shia, Bal ma shi Ahlussunna NE.

Madogarata itace: Manzon Allah ne da kansa yace sayyidnah Aliyu sunni ne ba shiey  ba. In da yake cewa:عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين عضوا  عليها باالنواجذ.   Maana na horeku da rike sunnata da kuma sunnar khalifofina Shiryayyu kuma masu shiryarwa ku cijeta da hirorinku.

Acikin wannan hadisi Wanda ya inganta kuma mashhurine ga bakunan musulmi Wanda bai bukatar takhriji, zamu fahinci Manzon Allah Ya kira khalifofinsa da cewa Ahlussunna NE, Wanda kuma sayyidnah Aliyu daya daga cikin khalifofin Annabi, to mi ya hada sayyidnah Ali da shia, balle har ace Idan ya bada ilmi an koya ne daga dan shia?

Babu alaka tsakanin kare da Liman.

Masu Sauraro sauran bayanin zai biyo baya, zan rika gutsurowa ne kadan kadan don gudun gajiyarda mai karatu. Allah Ya taimaki sunnah Annabi ya kuma rusa shia da mabiyanta.  خير .الكلام ما قل ودل

MASISJA NIGERIA 
30/05/2020

Comments

Har yanzu ni gaskiya Banga wani dalili na ilmi da Malam ya kawoba. Kamata yayi Malam yace Alh Adamu Lamama yace kaza akan Alkali Lawal Musa ga raddin abinda yace. Sannan Lamama yace Sayyadina Ali a.s dan shi'a ne yayi dogaro da kaza misali. Saboda mutum bazaice kawai wane Dan kazabane Babu abinda ya dogara dashi. Sai Malam yace nikuma nace Sayyadi Ali a.s Dan Sunnah be kuma ga madogarata. Idan Malam bai saniba ya sani yanzu kome abuse take. Abinda zakayi shekara kana nemansa ko karatunsa yanzu cikin minti biyu zaka iya samunsa. Ko jahiline mutum idan yaso karatu da sanin abinda yakeso yasani zai iya sani cikin Yan mintuna. Allah yasa mu face.

Popular posts from this blog

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia ta gudanar da taro domin sanin makamar aiki

Makarantar Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia (MASISIJA) ta gudanar da muhimmin taro domin sanin makamar aikinta na yada da'awar maluman muslunci.  Ranar laraba 10/06/2020 wasu daga cikin jagororin wannan kungiya suka yi taro inda suka tattauna akan muhimman abubuwanda zasu taimaka masu a fagen aikinsu.  Watanni biyu da suka gabata kungiyar MASISJA ta shirya wata muhadara mai taken "Tambayoyi da Amsoshi" ta tsawon sati shidda (6) wadda Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia ke gabatarwa.  A cikin ikon Allah,  an gabatar da ta tsawon makonni hudu (4) sai cutar Covid-19 ta billo wanda hakan yasa hukuma ta dakatar da dukkanin wani taro domin samun kariya daga cutar.  To Allah da ikonsa kuma bayan cutar ta lafa a jihar Katsina, yanzu an cigaba da harakoki kamar yadda aka saba.  Saboda haka ne kungiyar MASISJA, a karkashin wannan mitin, ta shirya tsaf domin cigaba da muhadarar tsawon sati biyu wadda mata ne kadai za ayi wa banda maza ka...

MA'ANAR SHI'A DA MANUFOFINSU (001)

Wannan raddi ne zuwa ga Ado Lamama game da shirmenda yayi a matsayin raddi zuwa ga Malamin Sunnah Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia.  Daga: Sheikh Mustafa Mansur Jibia Da farko Inaso in fara da bayani akan minene shia.  Hakika shi'a kishiyar sunnah ce ta fuskar akida.  Sunnah tana nufin addinin da manzon Allah Ya zo dashi kuma mai yin irinsa ya yarda da sahihancin sayyidnah Abubakar, umar, Uthman da Aliyu, tareda gamsuwa da tsarkin dukkanin matayen manzon Allah, gami da yarda da cewa duk sahabbai adalai NE. To wannan shine atakaice maganar Sunnah, kuma kishiyar hakan to shine shia, kamar kudurce cewa sayyidnah Abubakar, umar da uthman mutanen banza ne kuma yan wuta, sannan matan manzon akwai na banza acikinsu, musamman Nana Aisha Da Nana Hafsah sannan hadi da kafirta wani adadi na sahabban manzon Allah. To idan masu sauraro Sun fahinci banbance babancen to akan hakane zan gina raddi na akan rubutun da akayi.  Don haka a biyo don ...

Ya kamata a dinga tabbatar da sahihancin labari kafin a yada - Sheikh Sabi'u Jibia

Sheikh Ibrahim Sabi'u ya yi kira ga 'yan Social Media da su dinga tabbatar da Ingancin labari kafin su yada shi. Mataimakin shugaban majalissar ta kungiyar JIBWIS dake tarayyar najeriya Sheikh (Barr) Ibrahim Sabi'u Jibia, a yayin da yake gabatar da khudbar sallar juma'a yayi kira  ga masu amfani da kafafen sadarwar zamani (Social Media) su guji yada sharri da labarin karya. Ya kara da cewa: yana da kyau mutane  su dinga bincike domin tabbar da ingancin labari kafin su yada shi don gudun aikata abinda zai sa mutum ya wayi gari yana mai ladama game da abinda ya aikata. Kazalika ya karanto ayoyi daga  alqur'ani mai girma da hadisan Annabi (S.A.W) wadanda suke magana akan haramcin yin irin wannan mummunan aiki, wanda yin haka babban abin kyama ne a wajen Allah madaukakin sarki. A cewarsa tsawon lokaci da ya gabata akan samu batagarin malamai ne masu karantar da hadisan karya a yayin da suke karantar da dalibansu, amma yanzu zamani ya canza, kana kwance a gida za kai ta ...