Raddi na biyu zuwa ga Ado Lamama game da shirmenda yayi a matsayin raddi zuwa ga Malamin sunnah Alkali Sheikh Lawal Musa Jibia.
Daga: Sheikh Mustafa Mansur Jibia
Ado ya ce: sayyidnah Aliyu dan shia ne, ni kuma nace sam babu alaka tsakanin sayyidnah Aliyu da shia, Bal ma shi Ahlussunna NE.
Madogarata itace: Manzon Allah ne da kansa yace sayyidnah Aliyu sunni ne ba shiey ba. In da yake cewa:عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين عضوا عليها باالنواجذ. Maana na horeku da rike sunnata da kuma sunnar khalifofina Shiryayyu kuma masu shiryarwa ku cijeta da hirorinku.
Acikin wannan hadisi Wanda ya inganta kuma mashhurine ga bakunan musulmi Wanda bai bukatar takhriji, zamu fahinci Manzon Allah Ya kira khalifofinsa da cewa Ahlussunna NE, Wanda kuma sayyidnah Aliyu daya daga cikin khalifofin Annabi, to mi ya hada sayyidnah Ali da shia, balle har ace Idan ya bada ilmi an koya ne daga dan shia?
Babu alaka tsakanin kare da Liman.
Masu Sauraro sauran bayanin zai biyo baya, zan rika gutsurowa ne kadan kadan don gudun gajiyarda mai karatu. Allah Ya taimaki sunnah Annabi ya kuma rusa shia da mabiyanta. خير .الكلام ما قل ودل
MASISJA NIGERIA
30/05/2020
Comments