Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2020

SAKON BARKA DA SHIGOWA CIKIN WATAN AZUMIN RAMADANA~SHEIKH SABI'U JIBIA:

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatu. Ni Ibrahim Sabi'u Jibia, ina mika Godiyata ga Allah madaukakin sarki mai kowa da komai, wanda ke rayawa da kashewa, kuma wanda shine ya kar6i rayuwar mutane da dama wadanda sun ga azumin shekarar data gabata amma kuma bai basu damar ganin na bana ba. Mu da Allah yasa muka samu  damar ganin rayuwarmu a cikin wannan wata mai tarin darajoji, ina roka mana Allah mabuwayi yasa muyi ibada kar6a66iya, kuma yasa mu amfanu da dukkanin ni'ima da rahmar da yake yiwa bayinsa mu'munai, kuma yasa ranar lahira mu zamo a cikin 'yantattun bayinsa. Daga karshe inaa rokon Allah ya kawo mana karshen wadannan cututtuka da muke  fama dasu, da fatan Allah yasa mu cika da imani . Masisja Nigeria 27/04/2020

AN SALLAMI SHEIKH BARR. IBRAHIM SABI'U DAGA ASIBITI:

Godiya ta tabbata ga Allah mabuwayi da daukaka, wanda a cikin ni'imarsa da tausayinsa da amincewarsa ya jarabce ni da rashin lafiya, har ga shi yau kuma ya bani lafiya na baro gadon likita na dawo gida. Ina amfani da wannan dama domin godewa Allah madaukakin sarki tare da nuna jinjinata ta musamman ga 'yan uwa da abokan arziki da suka taya ni da addu'o'insu, ina rokon Allah ya saka wa kowa da alkhairi. Marassa lafiya Allah ya basu lafiya, masu lafiya Allah ya kara masu lafiya, wandanda suka rigaye mu gidan gaskiya Allah yajiqansu da rahama, idan lokacinmu ya yi Allah yasa mu cika da imani Amin.

LAAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH:

Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u Jibia, muna addu'a Allah yakara maka lafiya da nisan kwana domin amfanuwar al'ummar muslunci, kuma yasa zazza6in yazamo kaffara a gareka. Yanzu haka shehin malamin yana kwance a gadon asibiti, kuma jikin nasa da sauki, ana sa ran nan bada jimawa ba za'a sallame shi. Muna fatan zaku saka shi a cikkin addu'o'inku. ✍️Abdulrazak Ahmad Jibia Chairman: Masisja Nigeria.

SHEIKH BARR. IBRAHIM SABI'U JIBIA YA JA HANKULLAN 'YAN UWA MUSULMI DA SUBI UMARNIN SHUGABANNI:

Mataimakin Shugaban Majalissar Malamai ta kungiyar JIBWIS dake tarayyar najerya, Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u "Sarkin Malaman Jibia", ya ja hankullan 'yan uwa musulmi da subi umarnin shugabbani madamar bai saba wa addinin musluncii ba. Ya ce bai kamata talakawa/mabiya suyi jayayya da abinda hukuma tayi umarni a matsayin maslaha ga al'umma ba. Ina jawo hankulla musamman na 'yan uwa Malamai da Almajirai cewa ita tafiya ta addinin muslunci dole sai anyi biyayya ga Allah da Manzonsa da kuma hukuma, da abinda yake maslaha ga al'umma. Idan aka umarcemu da aikata wani abu ko kaurace masa, to kada ya zamo matsala, saboda duk abinda aka ce kada ayi a wannan yanayin magana ce dake nuna ba'a bukatar taron jama'a a wurin. Maganar sallar juma'a da aka  a dakatar da yinta a masallamatan juma'a ba matsala bane saboda babu Wanda aka hana yaje gida yayi. Saboda haka ina kara jawo hankullan 'yan uwa na Almajirai cewa kada mutum ya dauka idan y...

MUNZO KARSHEN KARATUNMU NA LITTAFIN MINHAJUL MUSLIM:

Sheihk Batista Ibrahim Sabi'u "Sarkin Malaman Jibia" ya kammala karatun littafi mai suna Minhajul Muslim, Wanda yake karantar da dalibansa lokaci-bayan lokaci: Za ku iya sauke wasu daga cikin karatuttukan na Audio akan wayoyin domin sauraro: Dannan LINK din duk wanda kuke bukata domin saukewa a wayoyinku ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ (1) Tunatarwa game da Azumi๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/73354 (2) Raino๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87221 (3) Gado๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87223 (4) Zihari da Li'ani๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87222 (4) Ajali๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87224 (5) Iddah da rabe-rabenta๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87227 (6) Khul'i da Ilaa'i๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87226 (7) Masu Gado Maza da Mata๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87228 (8) Saki 1๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87229 (9) Saki 2๐Ÿ‘‡ https://web.darulfikr.com/s/87230 (10) Hadarin Kashe Mummuni๐Ÿ‘‡ https://web.daru...

BARISTA IBRAHIM SABI'U JIBIA YA YI KIRA GA 'YAN KASUWA DASU SAUKAKA FARASHI A CIKIN WATAN AZUMI:

Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia Mataimakin shugaban majalissar malamai ta kungiyar Izala dake tarayyar najeriya Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u Jibia ya yi kira ga 'yan kasuwa dasu saukaka farahin kowane irin nau'in kaya musamman a cikin watan azumin ramadana. Ya ce ana bukatar kowane musulmi yayi koyi da shugaban halittu Annabi Muhammad (S.A.W) wajen yawaita taimako da bada tallafi ga Marayu, Gajiyayyu, da sauran mabukata, domin a cikin watan azumi ne Allah ke gafartawa bayinsa. Ya kara da cewa yana da kyau 'yan kasuwanmu su kara saukaka farashi hatta wandanda ba musulmai ba su amfanu da romon azumin watan ramadana, saboda manzom tsira (A.S) ya kasance mai fadada kyauta a acikin watan azumi duk da cewa shi mutum ne mai yawan kyauta a koda yaushe. Sannan ya yi kira ga masu rike da mukami na siyasa dana sarauta gami da attajirai cewa suji tsoron Allah su jajirce wajen taimakawa na kasa dasu domin karfin da Allah yayi masu. Kazalika suma talakawa ba'a barsu a ba...